Jummaʼa 30 Oktoba 2026 - 15:33
Sojojin Iran Za Su Mayar da Martani Mai Ƙarfi Kan Ƙawanyar Abokan Gaba Bisa Tsarin Lokacin da Aka Kayyade

Hauza/ Shugaban Hukumar Kare Ƙasa daga Barazanar da Ba Ta Soja Ba ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya jaddada cewa ƙasar ba za ta amince da killace ta ta ruwa, sama da ƙasa ba. Ya kuma bayyana cewa dakarun ƙasar za su mayar da martani mai ƙarfi kan wannan mataki na abokan gaba bisa jadawalin lokacin da aka tsara.

A cewar wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Birgediya Janar Gholamreza Jalali, shugaban Hukumar Kare Ƙasa daga Barazanar da Ba Ta Soja Ba, ya bayyana hakan ne yayin ziyararsa a birnin Qum, a wajen ganawarsa da wasu malamai da kuma tattaunawarsa da manema labarai.

Ya ce: “Dakarun sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za su amince da killace ƙasar ta ruwa, sama da ƙasa ba. Za su mayar da martani kan wannan killacewa bisa jadawalin lokacin da sakataren Majalisar Ƙoli ta Tsaron Ƙasa ya tsara.”

Da yake magana kan matakan abokan gaba, Janar Jalali ya ce, saboda gazawarsu a fagen yaƙi, sun koma ƙara tsaurara takunkumin tattalin arziki. Ya bayyana cewa, sakamakon sauyin salon barazanar da suke yi da kuma mayar da hankali kan matsin lamba ga al’umma, akwai buƙatar jama’a su yi amfani da kayayyaki cikin hikima, su guji almubazzaranci, tare da haɗa kai da gwamnati wajen tafiyar da yanayin yaƙi.

Ya ƙara da cewa, abokan gaba sun fahimci cewa ƙarfin sojojinsu bai yi tasiri ba wajen tunkarar martanin da Iran ke mayarwa ta hanyar makamai masu linzami, ayyukan ruwa da jiragen sama marasa matuƙa, da kuma haɗin kan al’umma wajen juriya. Saboda haka, suna ƙoƙarin matsa wa jama’a da shugabanni ta hanyar tsaurara matsin tattalin arziki, yaɗa tsoro da kuma yaƙin tunani.

Shugaban hukumar ya kuma jaddada cewa dakarun sojin ƙasar a shirye suke su mayar da martani ga duk wata barazana. Ya ce, a ɓangaren hukumomin gwamnati, gwamnati da Hukumar Kare Ƙasa daga Barazanar da Ba Ta Soja Ba suna haɗin gwiwa domin tabbatar da ci gaba da gudanar da muhimman ayyukan ƙasa. Hakan zai taimaka wajen gyara duk wata lalacewa da za ta iya faruwa ga muhimman ababen more rayuwa, tare da dawo da ayyuka yadda ya kamata cikin mafi ƙarancin lokaci.

Ya bayyana samar da wadataccen abinci da kuma ci gaba da ayyukan da jama’a ke buƙata a matsayin wasu daga cikin muhimman abubuwan da ake ba fifiko. Ya ce tabbatar da dorewar ayyukan jama’a da kuma kyakkyawan tsarin sarrafa albarkatu na daga cikin ayyukan da ya kamata a gudanar da su da muhimmanci a lokacin fuskantar barazana.

Haka kuma, Janar Jalali ya yi magana kan rawar da jama’a za su taka wajen kare tattalin arzikin ƙasa. Ya ce jama’a za su iya taimaka wa gwamnati wajen sarrafa albarkatu da rarraba ayyuka yadda ya kamata ta hanyar kula da amfani da ruwa, wutar lantarki da iskar gas, musamman idan aka yi la’akari da illar da aka yi wa wasu muhimman ababen more rayuwa.

Ya kuma jaddada muhimmancin guje wa almubazzaranci wajen amfani da kayan abinci, tare da kauce wa tara kayayyaki a gidaje ba tare da wata buƙata ta musamman ba. A cewarsa, amfani da albarkatu cikin tsari da kuma ɗaukar matakin da ya dace wajen sarrafa su na daga cikin hanyoyin da jama’a za su nuna haɗin kai a fagen kare tattalin arziki.

A ƙarshe, shugaban Hukumar Kare Ƙasa daga Barazanar da Ba Ta Soja Ba ya yi nuni da sanarwar da aka bayar cewa mutane miliyan 35 sun bayyana shirinsu na sadaukar da rayukansu domin ƙasarsu. Ya ce wannan shiri na sadaukarwa zai iya bayyana kansa a fagen tattalin arziki ta hanyar kula da yadda ake amfani da kayayyaki, taimaka wa gwamnati da kuma haɗin kan jama’a wajen tabbatar da ɗorewar ayyukan ƙasa.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha